A yau Juma'a shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a kudurin dokar fitar da kudi dala biliyan 8 da miliyan 300, domin ayyukan gaggawa na yaki da cutar Coronavirus ta COVID-19, kwana daya bayan da aka tabbatar da cewa cutar ta bazu zuwa wata unguwa dake kusa da fadar White House.
Kudurin dokar ya bi ta majalisar dattawa da ta wakilai, wadanda duk suka amince da shi.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa Richard Shelby, ya ce “a yanayi irin wannan, yayi amanin cewa, ba wani adadin kudi da za a ce yayi yawa a sha’anin kare Amurkawa.
Sakataren kiwon lafiyar al’umma na Amurka, ya fada a jiya Alhamis cewa, ana sa ran na’urorin gwaje-gwajen cutar kimanin miliyan daya za su isa dakunan gwaje-gwajen Amurka zuwa karshen makon nan.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka