Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Yi Fito Na Fito Da Canada Ta Fuskar Kasuwanci


Jiya Talata shugaba Donald Trump da sakataren kasuwanci Wilbur Ross sun ce ba su tsoron yin fito na fito da kasar Canada ta fuskar kasuwanci, bayan da Amurka ta dau matakin ladabtarwa kan cinikin katako da madara.

"Sun jibga mana kayansu a nan Amurka," a cewar Trump, wanda ya kara da cewa, "Mutane sun kasa gane cewa Canada ta jima ta na kwarar Amurka... sun yi shekara da shekaru su na wayo ma 'yan siyasarmu."

Trump ya kara da cewa ya na so a labta ma katako da madarar Canada haraji.

Ya yi wannan kalamin ne a wata ganawa da manoman Amurka, inda ya yi amfani da ikonsa na Shugaban kasa wajen rattaba hannu kan umurnin da ya bayar kan bangaren noma da kuma yankunan karkara.

Trump ya kuma yi magana da Firaministan Canada Justin Trudeau jiya Talata. "Shugaba Trudeau yayi watsi da zarge-zargen nan marsa tushe da Ma'aikatar Cinakayyar Amurka ta yi da kuma matakin rashin adalci da aka dauka na saka haraji," a cewar bayanin Fadar Shugaban na Canda.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG