Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Kawo Karshen Yakin Da Takeyi A Kasar Yemen


A Ranar Laraba Majalisar Dattawan Amurka Suka Jefa Kuri'a, Domin Kawo Karshen Yakin Da Amurka ke yi a Yemen, Wanda Kasar Saudiyya Ke Jagoranta.

Majalisar dattawan Amurka ta jefa kuri’a jiya Laraba, akan yin dokar kawo karshen yakin da Amurka ke yi a Yemen, wanda kasar Saudiyya ke jagoranta, ‘yan majalisu 63 ne suka goyi bayan matakin, 37 kuma basu amince ba.

Kuri’ar da aka jefa yawanci wata alama ce ga gwamnatin kasar, saboda shugabannin jam’iyyar Republican ba su nuna alamun sun yi na’am da matakin ba.

Wannan kuri’ar da suka jefa wata hujja ce dake nuna barakar dake tsakanin fadar White House da ‘yan majalisar dokokin Amurka game da kasar Saudiyya, duk da cewa manyan jami’an shugaba Donald Trump, a fannin tsaron kasa su biyu, sun gabatar da muhimman bayanai gaban majalisar dattawan.

Kusan watanni biyu bayan da aka kashe wani dan jaridar kasar Saudiya, mai caccakar Yariman masarautar kasar a karamin ofishin Jakadancin Saudiyya dake Santanbul.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da sakataren tsaron kasar Jim Mattis, sun yi kira da a kula da dadaddar dangantakar kud-da-kud dake tsakanin Saudiyya da Amurka. Ciki, harda gudunmuwar da Amurka ke badawa a yakin da Saudiyyar ke jagoranta a Yemen.

A wani lamari na daban, wasu hare hare ta sama da dakarun Saudiyya ke jagoranta suka kai akan mayakan Houthi, sun hada da makaman da aka siyo daga Amurka. Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar dubban fararen hular Yemen, sun kuma lalata asibitoci tareda ratattaka wasu unguwanni.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG