Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka zata mikawa Afrika ta Kudu aikin yaki da cutar kanjamau


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton
Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Washington ta fara mikawa Afrika ta Kudu ikon gudanar da ayyukan yaki da cutar kanjamau, kasar da tafi kowacce a duniya yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV.
Clinton ta sanar da haka ne yau Laraba yayin jawabinta a jami'ar Western Cape dake bayan garin birnin Cape Town. Ta bayyana cewa, yarjejeniyar wani gagarumin ci gaba ne a yaki da cutar kanjamau.

Amurka ta rage yawan kudin da take badawa na yaki da cutar kanjamau zamanin shugaba Thabo Mbeki wanda ya musanta cewa, akwai dangantaka tsakanin kwayar cutar HIV da cutar kanjamau, ya kuma ki amincewa da magungunan jinyar cutar da kasashen duniya suka yi na’am da shi.

Washington ta kashe dala biliyan uku da miliyan dubu dari biyu, tun daga shekara ta dubu biyu da hudu, kan ayyukan yaki da cutar kanjamau a Afrika ta Kudu. Ko da yake kasar ta taka rawar gani a wajen rage yada cutar, sama da kashi goma sha bakwai bisa dari na al’ummar kasar suna dauke da kwayar cutar HIV
XS
SM
MD
LG