Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Sakawa Masu Rikincin Sudan ta Kudu Takunkumi


Salva Kiir shugaban Sudan Ta Kudu
Salva Kiir shugaban Sudan Ta Kudu

Sakataren Harkokin Wajen Amurka yace kasarsa tana tunanin kakabawa wadanda ta kira masu tada zaune tsaye a Sudan Ta Kudu takunkumi

Sakataren harkoki wajen Amirka John Kerry, yace Amirka tana nazarin azawa mutane dake rurutar wutar rikicin a kasar Sudan ta kudu takunkunmi, inda tarzomar da ake yi tasa fiye da mutane miliyan guda rasa matsuguninsu.

A wata hira da Muryar Amirka tayi da shi jiya Litinin a ma'aikatar harkokin wajen Mr Kerry yace gwamnatin Amirka tana nazari sosai tana duba yiwuwa aza takunkunmin, kodayake ya fito takamame ya fadi wanda Amirka zata auna ba.

Yace yayi imanin cewa fadan da ake yi a kasar Sudan ta kudu da ya yiwo asali daga rikicin mai da neman iko da kuma gabar kabilanci ya bude da zama wani abu dabam.

A tsakiyar watan disamba fada ya barke lokacinda shugaba Salva Kir ya zargin tsohon mataimakinsa Reik Machar da laifi kokarin yi masa juyin mulki. Joh Kerry yace rikicin na kasar Sudan ta kkudu bala'i ne, musamma idan aka yi la'akari da yadda kasa ta dade tana fafitukar ganin ta samu yancin ci gashin kai.

Gobe Laraba idan Allah ya kaimu sakataren harkokin wajen na Amirka zai fara ziyara a kasashen gabashin Afrika. Zai je Addis Ababa baban birnin kasar Ethiopia inda shawarwarin da ake yi tsakanin wakilan gwamnati dana yan tawayen kasar Sudan ta kudu suka kasa samun ci gaba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG