Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talauci: Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya


A woman sits in a canoe with her child as the government begins the demolition of homes in Legas.

A cikin shekaru biyar masu zuwa Amurka za ta taimakawa Najeriya da dala miliyan biyu da dubu dari uku ko nera biliyan 460. Manufar tallafin shi ne domin a kawar da talauci a duk fadin kasar ta Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ta Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo shi ya sanya hannu a madadin Najeriya yayin da daraktan hukumar raya kasashe masu tasowa ko USAID resshen Najeriya Michelle Harvey ya sa hannu a madadin gwamnatin Amurka.

Shirin zai lashe sama da dalar Amurka miliyan biyu ya biyo bayan alkawarin da Amurka ta yiwa Najeriya yayin ziyarar da shugaba Buhari ya kai Amurka a watan Yuli.

Shirin nada zummar marawa Najeriya ta rage matsanancin talauci mai radadi cikin yanayin tsarin dimokradiya wanda zai karfafa tayar da komadar tattalin arziki. Taimakon zai samarda al'umma mai cike da koshin lafiya da kuma karfafa kyakyawan shugabanci na gari.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG