Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zatayi Nazarin Goyon Bayan Rundunar Hadin Gwiwa Da Saudi Ke Jagoranta


Farmakin da rundunar hadin gwiwa suka kaiwa wajen jana'iza
Farmakin da rundunar hadin gwiwa suka kaiwa wajen jana'iza

Fadar White House ta shugaban Amurka tace gwamnatin shugaba Obama zata fara nazarin goyon bayan da take baiwa yakin da rundunar hadin guiwa ta sojan kasa da kasa a karkashin jagorancin Saudi Arabia ke gudanarwa a kasar Yemen.

Biyo bayan wani farmaki ta sama akan taron wasu masu halartar wata jana’iza, inda har aka hallaka sama da mutane 140 a birnin Sana’a kuma akalla mutane 500 suka jikata.

A wata sanarwa da yammacin Asabar, kakakin majalisar tsaron Amurka, Ned Price, yace Amurka tana bakin cikin ainun a kan wannan farmakin a kan mutanen dake halartar jana’izar, abinda ke nuna ci gaban karin kai irin wadanan hare haren a kan fararen hula a Yemen.

Ita ma gweamnatin Saudiyya ta fada a jiya Lahadi cewa zata kaddamar da nata bincike akan yadda wannan al’amarin ya faru.

Izuwa yanzu babu wani cikakken bayani a kan abubuwan dake kunshe a cikin wannan farmakin. Amma dai rahotannin sun nuna cewa ma’aikatar agaji sun yi amfani da buhuhuna suna tattara gabobin daruruwan mutane da suka tarwatse a wannan farmakin a nan zauren zaman makokin da kuma wajen ginin.

Akasarin wadanda sukabada bayanai gameda wannan harin sun ce anyi asaran rayukkan ne a sanadin wani roka mai linzame da wani daga cikin jiragen saman yakin ya cillo ne, kuma wannan shine farmaki mafi yin barna tun lokacin da Saudiya ta fara wannan yaki a Yemen a cikin watan Maris 2015.

Hukumomin Saudi Arabia dai sun musunta cewar suna da hannu a wannan harin, koda yake wani rahoto yace mai yiyuwa ne ba za’a rasa hannun ‘yan kunar bakin wake a cikin wannan harin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG