Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa sun gudanar da hidimomin tunawa da juyowar ranar da aka kaiwa kasar harin ta'addanci


Shugaban Amurka Barack Obama, da maidakinsa Michelle Obama, tare da ma'aikatan fadar White House
Yau dubban mutane sun taru a biranen New York da nan Washington don gudanarda hidimomi iri-iri na tuna sake juyowar ranar 11 ga watan Satumbar 2011, ranar da hare-haren ta’addancin da aka kawowa Amurka suka hallaka mata kusan mutane 3,000.

A fadar White House, shugaba Barack Obama da matarsa Michelle da sauran muhimman mutane da dama duk sun durkusar da kawunansu, suka yi tsit da karfe 8.46 na safe, wanda a wannan lokacin ne, ran 11 ga watan Satumbar na 2001, jirgin farko ya fara abkawa akan babbar cibiyar ciniki ta duniya dake can New York. An shirya cewa daga baya shugabannin na Amurka zasu yi jagorancin irin wannan hidimar tunawa din a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, wurin da jirgi na ukku ya abkawa a lokacin hare-haren na 2001.

Shi kuma mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai je yayi jawabi ne a kauyen Shkasville dake jihar Pennsylvania inda a nan ne jirgi na hudu ya faado bayanda pasinjojin dake cikinsa suka yi gumurzu da ‘yan ta’addar da ke cikinsa, suna kokarin juyo da shi zuwa hanyar Washington.

Tuni ma sakataren tsaron Amurka, Leon Panetta ya ziyarci kauyen na Shaksville, inda yayi kira da cewa kada a rinka mantawa da wadanda suke raye, suna bautawa kasar nan inda ya bayyana cewa “Babbar damuwata shine cewa har yanzu bama nuna cikakkiyar kulawa da maida hankali ga wadanda har yanzu suke ci gaba da yaki da kuma rasa rayukkansu don wannan kasa. Har yanzu muna ci gaba da rasa mutanenmu maza da mata a Afghanistan, mutanen da kullum suke gitta rayukkansu don kasancewar wannan kasa da tabattarda cewa ta ci gaba da zama a cikin kariya.”

Kamar yadda aka yi a shekarun da suka gabata, a yau ma iyalin wadanda abin ya shafa zasu shiga cikin karatun sunayen wadanda aka rasa din da za’a yi a wurin da ake kira “Ground Zero”, watau mazaunin su wadanan tagwayen gine-ginen biyu na Cibiyar Ciniki ta Duniya da wadanan jiragen biyu suka ragargaza.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG