Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa suna bukin cika shekaru 235 da samun 'yancin kai


Tutar Amurka

Yau Amurkawa suke bukin samun ‘yancin kai ranar da ake kira hudu ga watan Yuli.

Yau Amurkawa suke bukin samun ‘yancin kai ranar da ake kira hudu ga watan Yuli. Amurkawa suna bukin ranar da kakaninsu suka ayyana ‘yancin kai daga Birtaniya a shekara ta dubu da dari bakwai da saba’in da shida tare da fareti da wassani iri iri da kuma cin abinci. Za a yi wasannin wuta jiya da dare a manyan biranen kasar da suka hada da Washington DC da NY da Philadelphia, inda aka sa hannu a yarjejeniyar ‘yancin kan. Za a rantsar da mutane dari a matsayin sababbin ‘yan kasa a Mount Vermon inda shugaban Amurka na farko George Washington ya fito. Shugaban kasa mai ci yanzu Barack Obama zai karbi bakuncin sojoji da iyalansu a wani zaman cin abinci da wasannin kade-kade da za a yi a fadar White House

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG