Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Da Belin Abdulrashid Maina


A Najeriya, Kotu ta bada umarnin sako Tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho Abdulrashid Maina bayan ya shafe tsahon wata tara a tsare.

Tun ranar 26 ga watan Nuwamban 2019, kotun tarayya da ke Abuja a karkashin Mai Shari'a Okon Abang ta bayar da belin Abdulrashid Maina, amma rashin cika sharrudan bayar da shi beli suka sa aka cigaba da tsare shi a kurkuku.

Daga bisani lauyoyinsa suka roki a sassauta masa sharrudan belin, inda alkali ya yarda ya rage yawan Sanatoci da za su karbi belin sa zuwa guda daya.

Barista Mazi Afam Osigwe daya daga cikin lauyoyin da ke kare Maina ya fada wa VOA ta wayar tarho cewa ba a cika sharrudan belinsa ba sai da Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar yankin da Maina ya fito ya zo ya tsaya masa sannan aka bada belin sa ranar Juma'a 24 ga wannan wata na Yuli.

Mazi ya kara da cewa ba a sako shi ba sai da aka cika wasu takardu wajen bin wasu hanyoyi da ka'idojin aiki sannan aka sako shi, kana wanda ya ke wakilta yanzu haka yana zaune cikin iyalansa.

Sannan ya ce za’a cigaba da shari’ar idan kotu ta dawo hutu a cikin watan Satumba mai zuwa.

ABUJA: Sabon ginin EFCC
ABUJA: Sabon ginin EFCC

A ranar 25 ga watan Oktoban 2019, Hukumar EFCC ta gurfanar da Abdulrashid Maina tare da dansa Faisal da wani Kamfani mai suna Common Input Property and Investment Ltd a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a karkashin Mai Shari'a Okon Abang inda ya ke fuskantar tuhumar cin hanci, rashawa da yin sama da fadi da biliyoyin Naira.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG