Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Baiwa Gwamnatin Tarayya Wa'adi Kan Cin Zarafin Dan Jarida A Kaduna


Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbanjo.

Ana zargin 'Yansanda sun ci zarafin wakilin gidan rediyon Deutsche Welle dake kaduna a wata zanga-zangar 'yan shi'a.

An baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin mako daya ta maidawa wakilin Sashen Hausa na gidan Rediyon Deutsche Welle a Kaduna Ibrahima Yakuba, kayan aikinsa da aka lalata.

Wata kungiyar kare ‘yancin Bil’Adama da ake kira da cibiyar wanzarda zaman lafiya da adalci a Afirka wacce ta bada wannan wa’adi, tace bai kamata a rika cin zarafin ‘Yan jarida ba.

Shugaban cibiyar Dr. Suleiman Shu’aibu Shinkafi, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai da kngiyar ta kira a Jos yace, ‘yan jarida sune ido da bakin talakawa.

Ana zargin wakilin ya hadu da fushin ‘Yansanda a kaduna, lokacinda yake daukar bayanai a wata zanga-zanga da take son ta rikida ta zama arangama tsakanin ‘yan shi’a da jama’ar gari.

Shima da yake magana, shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jahar Flato Yakubu Tadi, yace akwai bukatar uwar kungiyar ta kasa ta sa baki cikin wannan batu. Domin idan ba haka ba, wannan somin tabi ne kamin shekara ta 2019 lokacinda za’a yi zaben kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG