Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayar Da Rahoton Karancin Burodi A Babban Birnin Kasar Zimbabwe


Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da Firayim Minista Morgan Tsvangirai

Kafofin yada labaran gwamnati a Zimbabwe sun bayar da rahotannin karancin burodi a babban birnin kasar, inda wani babban kamfanin yin burodi ya daina aiki a wannan satin.

Kafofin yada labaran gwamnati a Zimbabwe sun bayar da rahotannin karancin burodi a babban birnin kasar, inda wani babban kamfanin yin burodi ya daina aiki a wannan satin.

Kamfanin dillancin labaran Zimbabwe (ZBC) ya ce kamfanin yin burodi mai suna Lobel na fama da dinbin bashi, kuma zai daina aiki daga nan zuwa watanni biyu a sa’ilinda zai yi kokarin samo sabon mai daukar nauyinsa ta fuskar saka hannun jari.

ZBC y ace rufe kamfanin Lobel da wani gidan burodin kuma mai suna Superbake, ya kawo karancin burodi abirnin Harare.

Wata jaridar Zimbabbwe mai zaman kanta, mai suna News Day ta bayar da kiyasin adadin karancin burodin akan kwayar 150,000 kulluyaumin.

Zimbabwe ta sha fama da karancin abinci akai akai saboda dadaddiyar matsalar tattalin arziki cikin shekaru 10 da su ka gabata.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na dora laifin kan salon shugaba Robert Mugabe, musamman ma shirin nan na sauye-sauye game da batun gonaki, ta yadda aka kwace gonaki daga wurin fararen fatan da suka kwari kan noman zamani aka bai wa bakaken fata.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG