Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Sunan Maharin London


Yankin Westminster da aka kai hari a London
Yankin Westminster da aka kai hari a London

'Yan sanda a London sun bayyana sunan mutumin da ya kai harin London a matsayin Khalid Masood, wanda haifaffan Birtaniya ne.

Dan shekaru 52, Masood, mutum ne da 'yan sandan Birtaniya suka ce sun san sa bisa wasu laifuka da aka kama shi da aikata wa da suka hada da mallakar makamai a baya.

A shekarar 2003 an kama shi dauke da wuka, sai dai duk ba a same shi da laifin aikata ta'addanci ba.

Masood ya kai harin ne a gadar Westminitser inda ya bi ta kan mutanen dake tafiya a gefen hanya da mota, sannan daga baya ya shiga harabar Majalisar Dokokin Birtaniya ya caka wa wani dan sanda wuka.

Amma nan take wani dan sanda ya harbe shi har lahira yayin harin wanda ya faru a jiya Laraba.

Gabanin a bayyana sunansa, kungiyar IS ta dauki alhakin harin da ya kai da mota da kuma wuka, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku ciki har da wani dan sanda.

Wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na yada labarai, ta bayyana maharin a matsayin "sojan IS."

Sai dai kungiyar ba ta nuna ko ta taimaka wa mutumin wajen kitsa wa ko aiwatar da harin ba.

Amma sanarwa ta nuna cewa maharin ya amsa yekuwar da kungiyar ke yi na a kai hari akan fararen hula da kuma dakarun kasashen dake hada kai da Amurka suke yakar kungiyar ta IS.

Ya zuwa yanzu 'yan sandan Birtaniya sun cafke mutane takwas da ake zargin na da hanu a harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG