Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Makarantun Sakandare A Jihar Kano


A yau litinin aka bude makarantun sakandare a jihar Kano domin daliban da ke ajin karshe, don shirye-shiryen tunkarar rubuta jarabawar karshe da za’a fara kasa da makwanni biyu masu zuwa, wadda hukumar shirya jarabawa ta Afrika ta yamma wato WAEC da takwararta ta NECO ke shiryawa a kowacce shekara.

Tun a makon jiya ne wasu daga cikin jihohin Najeriya kamar jihohin Jigawa da Lagos suka bude nasu makarantun, bayan cimma yarjejeniya akan haka tsakanin hukumomin ilimi da babban kwamitin yaki da cutar Coronavirus na kasar.

Jumlar dalibai 27,464 ne daga makarantun gwamnati da na masu zaman kansu a jihar Kano za su rubuta jarabawar kammala karatun sakandaren, sai dai gwamnati ta hade cibiyoyin rubuta jarabawar mallakar ta zuwa 33 maimakon 199, kamar yadda kwamishinan ilimi na jihar Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Kiru ya shaidawa wakilin muryar Amurka.

Gabanin komawar daliban da ake sa ran zai wakana a yau Litinin, tun Juma’ar da ta gabata ne gwamnati ta kaddamar da aikin feshin kashe cuttuka da kwari a ajujuwa da harabar makarantun domin tarbar daliban.

Kwamishinan muhalli na Kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso, ya ce aikin ya kunshi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Baya ga feshi a makarantun, hukumomin jihar Kano sun ce za su raba takunkumin rufe baki da hanci ga daliban, tare kuma da samar da sinadarin wanke hannu da kuma na’urar auna zafin jikin bil’adama a dukkanin makarantun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG