Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Budewa Tawagar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Wuta Aka Kuma Tada Musu Nakiya


Jiya Talata an samu rohotanni dake karo da juna kan ko kwararun OPCW sun issa Douma. Tawagar tana son kai ziyara gurin da ake zargin an kai harin makaman guba ranar 7 ga watan Afrilun nan wanda ya kashe akalla mutane 40.

An budewa tawagar tsaron Majalisar Dinkin Duniya wuta aka kuma tada nakiya a daidai lokacin da suke kokarin gudanar da bincike da jirgin leken asiri a wani gari dake Syria lokacin da suke dakon ziyarar masu binciken makaman guba.

Da issar su zangon na farko, mutane dayawa sun taru, kuma shawarar da hukumar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta bayar ita ce, tawagar ta janye, bisa ga cewar shugaban kungiyar haramta amfani da makamai masu guba (OPCW) Ahmet Uzumcu jiya Laraba. zango na biyu kuma, tawagar ta fuskanci 'yan harbe harbe, aka kuma tada nakiya a gurin.

Yace lamarin ya faru ne jiya Talata kuma tawagar ta koma Damascus.
Majiya daga Majalisar Dinkin Duniya ta shaidawa VOA cewa, ba wani mamban tawagar da ya ji rauni lokacin aukuwar lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG