Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Dokar Kwarmata Labarin Safarar Mutane


Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

Hukumar yaki da fataucin mutane ta nemi mahukuntan kasar Najeriya da su samar da dokar da zata ba da daman kwarmata labarin safarar mutane tare da amincewa da bayar da tukwuici kamar yadda ake yi yanzu akan kudaden sata da makwarmata suke taimaka wa ana ganosu.

Kakakin hukumar dake yaki da fataucin ko safarar mutane ta Najeriya Mr Josiah Emerem ya bayyana makasudin samun dokar kwarmata labarin safarar mutane.

Yana mai cewa mutane da dama ba sa iya kai rahoton fataucin mutane kamar yadda a keyi da sauran laifuka. Rashin dokar na takaita ma hukumar samun rahotanni aika aikar da ake tafkawa a kasar.

Dokar kwarmata a bangaren cin hanci da rashawa da zarmiya da yiwa tattalin arziki zagon kasa na samun nasara sosai. Inji kakakin dalili ke nan da hukumarsu ta zabura ta nemi gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar domin a dinga kwarmata bayanai kan masu safarar mutane. Yin hakan zai karfafa 'yan Najeriya su ji karfin kwarmata wa hukumar bayanai.

Dr Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja yace matakin zai taimaka gaya wajen dakile fataucin mutane a Najeriya musamman a wasu jihohin kudancin kasar inda ake fita da yara mata waje a tilasta masu shiga karuwanci.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG