Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Saudiya Ta Kara Cibiyar Daukan Tambarin Yatsun Alhazan Najeriya


Mahajjata

A kokarin taimakawa alhazan Najeriya su saukar da aikin ibadar wannan shekarar hukumar alhazai ta bukaci Saudiya ta kara cibiyoyin daukar shaidar tambarin yatsun mutum kazalika an kira gwamnati ta ragewa alhazan farashin dala

Shugaban hukumar alhazan Najeriya Barrister Mukhtari Abdullahi Muhammad ya bukaci Saudiya ta kara cibiyoyin daukan tambarin yatsun alhazan Najeriya domin saukakawa alahazai 95,000 saukin samun biza.

Shugaban yana tattaunawa ne akan lamuran harkokin aikin haji a kafar gidan talibijan naMinara mallakar kungiyar IZALA, ya ce yanzu cibiyoyin daukan tambarin uku ne kacal. Inji shugaban gwamnatin Najeriya na tattaunawa da gwamnati Saudiya ta yadda alhazan Najeriya ba zasu sha wahala ba.

Shugaban gidan talibijan din Imam Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar ta kafa gidan talibijan din ne da zummar domin bunkasa addinin Islama da zaman lafiya a tsakanin al'ummar Najeriya. Ya kira gwamnati ta sake duba farashin dala ga aikin hajji.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG