Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Shugaba Buhari Ya Sauka Daga Mukamin Ministan Mai


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Wata kungiyar gamayya a jahar Kanon Najeriya ta bukaci Shugaban Najeriya kuma Ministan man kasar ya yadda kwallon magoron ya rabu da kuda. Ma'ana, ya sauka daga mukamin Ministan mai don kar ya raba hankalinsa; ya nada sabon Ministan mai. Wannan ya biyo bayan abin da masu wannan ra'ayin ke kira yawaitar matsalar mai.

A yayin da ga dukkan alamu abubuwa ke dada yin yawa ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kuma ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar karanci da kuma tsadar man fetur da kuma, uwa-uba, abubuwan da ke bin bayan tsada da kuma rashin man, gamayyar kungiyoyin sa kai a Kano sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta sauka daga kujerar Ministan Albarkatun Mai na kasar kuma ya nada wanda ya kamata domin tunkarar wannan matsala.

Su ka ce idan aka nada Ministan mai, za a san wanda za a tambaya idan aka samu matsala a maimakon Shugaban kasa, wanda akwai abubuwa da yawa gabansa.

A wani taron gaggawa dangane da halin da kasa ke ciki, kungiyoyin sun tattauna sauran batutuwa da suka shafi rayuwar Jama’a, musamman hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma yawaitar rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, lamarin da sukace na kara zama barazana ga makomar Najeriya.

Dr Muhammad Mustafa Yahya, Daraktan Kungiyar Democratic Action Group shine yayi Magana da manema labarai a madadin sauran kungiyoyin, kuma ya yi wa wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari Karin haske game da abubuwan da taron ya cimma. Ga dai kwari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG