Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Wata Mahayar Tsaunin Pakistan; Wani Ya Bace


Tsaunin Nanga Parbat

Ta sake faruwa da masu rungumar kaddarar nan su hau tsaunin Nanga Parbat na kasar Pakistan. Mahaya biyu sun makale a kan hanyarsu ta isa nisar mita sama da dubu takwas. Sun kira masu kai dauki amma kafin su iso, ba su ga namijin ba.

An sami wata ba-Faransa da ranta a kan tsaunukan arewacin Himalaya dinnan masu matukar hadari, wadanda ake kira, “Tsaunuka Masu Kisa,” to amma masu kai daukin sun kasa gano abokin hawa tsaunin na ta, dan asalin kasar Polond.

Mutanen biyu, Tomasz Mackiewicz daga Polond da kuma Elisabeth Revol daga Faransa, sun yi yinkurin hawa ne zuwa tsawon mita 8,126 na Nanga Parbat. To amma sai su ka makale a tsawon mita 7,400 don haka su ka yi amfani da wayar salula wajen kiran a kai masu dauki, a cewar kungiyar da ta shirya wannan gasar.

Ya kasance tilas ga wata tawagar mahaya tsauni daga kasar Polond ta dakatar da batun hawa tsaunin saboda a ceto mahaya biyun da su ka makale.\

Sojojin Pakistan ne su ka kai wasu mutane hudu daga tawagar ‘yan Polond din zuwa Nanga Parbat.

Da safiyar yau Lahadi aka bayyana ta kafar FaceBook cewa an gano Elisabeth Revol.

Daga bisani, Ludovic Giambiasi, daya daga cikin abokan Revol, ya bayyana ta kafar FaceBook cewa masu ayyukan ceto

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG