Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cigaba Da Fafatawa a Ukraine


Ukrainian soldiers sit on top of an APC after a Ukrainian check was attacked by pro-Russians near the village of Blahodatne, eastern Ukraine, May 22, 2014.

Juma'ar nan, an ci gaba da fafatawa tsakanin 'yan aware wadanda suke goyon bayan Rasha da sojojin gwamnati a gabashin kasar Ukraine, ana sauran kwanaki biyu ayi zaben shugaban kasa.

Shedun gani da ido da jami'an tsaro a birnin Kiev sun bada rahoton cewa, anyi arangamomi a biranen Semenouka da Rubizhima da kuma yankin Donetsk.

Jiya Alhamis da dare aka kashe sojoji goma sha uku a sakamakon harin da 'yan aware suka kai Donetsk.

Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon yayi Allah wadai da tarzomar, yana mai fadin cewa ya kamata bangarorin biyu suka kara zage dantse wajen tabbatar da an gudanar da zabe cikin yanci da adalci da kuma walwala.

Jami'an kasar Ukraine sun dorawa Rasha laifin kokarin rurutar wutar rikicin da kuma dagula zaben da za'a yi, zaben da Rasha ta yi dari darin marawa baya.

Shi kuma Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, a yau juma'a ya zargi kasashen yammacin duniya da laifin amfani da dabarun zamanin zaman doya da manja wajen shafawa Rasha kashin kaji.
XS
SM
MD
LG