Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar zaben jihar Plato ta tabbatar da rashin gudanar da zabuka a wasu rumfunan zabe ashirin a kananan hukumomi tara a jihar Plato, wadanda ta bada umurnin yin zaben a yau lahadi.

A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar zaben jihar ta Plato Mr. Osaretin Imahiyerobo, ya bayyana kananan hukumomin da suka hada da Kanam, Bassa, Jos ta gabas, Jos ta arewa, Wase, Kanke, Langtang ta kudu, Mangu da Riyom.

Mr. Oseratin yace matsalar ta biyo bayan tangarda da aka samu ta na’urar tantance katin zabe da kuma jinkirin da aka samu na kai kayan zabe kan lokaci. Jami’in hukumar zaben ya kara da cewa a yanzu haka basu sami sakamakon zabe ba saboda ba a kammala zabe a wasu rumfunan zaben ba.

Wasu da suka samu suka kammala zaben sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da zaben.

A jihar Nasarawa ma rahotanni na nuna cewa an kammala zabe lami lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG