Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Jituwar Kwance Damara Tsakanin Gwamnatin Sudan Ta Kudu Da 'Yan Tawaye


Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir

A wani al'amarin da wasu za su ce ba girin-girin ba ta yi mai, Gwamnatin Sudan Ta Kudu da 'yan tawaye, bayan gwabzawar da aka yi ta yi, sun cimma yarjajjeniyar tsagaita wuta tare da cigaba da aiwatar da wasu matakai na yada zaman lafiya tsakaninsu.

Gwamnatin Sudan Ta Kudu da kungiyoyin mayaka sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar tsagaita wuta jiya Alhamis, a yayin tattaunwar zaman lafiya a kasar Habasha, a yinkurinsu na baya-bayan nan na kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru hudu ana yi.

Yarjajjeniyar ta tanaji cewa zuwa gobe Asabar dukkan bangarorin za su kawo karshen gwagwarmaya da makami, su janye daga fagen daga, su saki fursunonin yaki, da ‘yan siyasan da ke tsare, da kuma mata da yaran da aka kama.

Ciyaman din Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya bayyana yarjajjeniyar da abin da ya kira, “matakin farko mai karfafa gwiwa,” a kokarin da ake na kawo karshen yakin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG