Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Takunkumin Hana Amfani Da Keke Mai Tayu Uku A Diffa


Wasu kekuna masu tay uku

Yayin da matsalar Boko Haram ke kara sauki, an saukaka ma masu amfani da kekuna masu tayu uku a jahar Diffa ta Janhuriyar Nijar.A yanzu ana iya amfani da kekunan a manyan garuruwan jahar.

Hukumomin jahar Diffa da kasar Nijar baki daya sun dage takunkumin hana amfani da keke mai tayu uku wanda wasu ke kira A Daidaita Sahu, bayan ziyarar Ministan Cikin Gida, Bazzum Muhammad, zuwa jahar ta Diffa a makon da ya gabata, inda ya marabci wasu ‘yan Boko Haram da su ka tuba.

Wannan sassaucin na da nasaba da alamar kyautatuwar al’amura a wannan jaha mai fama da kalubalen tsaro, musamman ganin yadda ‘yan Boko Haram ke ta mika wuya ga hukumomi.

Hasali ma, gwamnan Diffa, Mallam Dandano, ya yi karin bayani ta waya ga wakilinmu a Birnin Konni, Haruna Mamman, da cewa, “Sai mu ce mun gode Allah; Alhamdulillahi akwai sauki; kuma idan ka na da labari, Ministan Cikin Gida Bazzum Muhammad ya zo nan tarbar ‘yan ‘uwanmu da ada su ka bace cikin kungiyar Boko Haram, amma yanzu sun fara dawowa gida. Insha Allahu dai zaman lafiyan nan da ake nema zai samu. Kuma kasan ita harkar duniya komai ake yi ana neman sauki; don haka an ba da masu amfani da keke mai tayu uku izinin amfani da shi a Diffa, Maine, Gingimi da sauran manyan garuruwa – su yi ta gudanar da harkokin sana’a da kasuwancinsu. Akwai ka’idojin da za a gindaya kamar yin takardu da sauransu don tabbatar da tsaro. Mu na so mutane su samu kwanciyar hankali wajen gudanar da harkokinsu, kuma insha Allahu mutane za su ji dadin wannan matakin.”

Gwamnan na Diffa ya ce ‘yan Nijar da ke ficewa daga Boko Haram na karuwa. Sannan ya yi kira ga duk masu ‘yan’uwa cikin kungiyar ta Boko Haram da su kokarta su shawarce su su dawo daga rakiyar wannan kungiyar.

Ga wakilinmu Haruna Mamman da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

XS
SM
MD
LG