Accessibility links

Jami'ai a kasar Ivory Coast sunce sun dakile yunkurin juyin mulki da wasu jami'an soja wadanda suke gudu hijira ciki harda Kanal Kate Gnatoa, wanda shine shugaban ayarin suka yi shirin yi

Jami'an kasar Ivory Coast sunce sun dakile yunkurin juyin mulki da wasu jami'an soja wadanda suke gudun hijira suka shirya yi, ciki harda kanal Kate Gnatoa wanda shine shugaban ayarin.

Talata da dare Ministan harkokin cikin gidan kasar ya fada a gidan talibijin na kasar cewa hukumomi su kama mutane da dama ciki harda Kanal Gnatoa, wanda aka ce shine shugaban ayarin sojojin.

Gidan talibijin ya nuna hoton vidiyon sojoji da dama cikin rigar soja, a yayinda daya daga cikinsu yake karanar sanarwar cewa Majalisar mulkin soja ta kwace mulki.

Ministan harkokin cikin gidan na Ivory Coast yace da hannun Lida Kouassi, tsohon Ministan tsaron kasar a shirya makarkashiyar yin juyin mulki.

A zaben shekara ta dubu biyu da goma shugaba Alassane Ouattara ya kada tsohon shugaba Gbagbo, amma tsohon shugaban yaci gaba da yin kememe akan mulki. Kimamin mutane dubu uku aka kashe a mumunar fafitukar neman mukami da aka yi tsakanin bangarorin biyu, har zuwa lokacinda aka kama tsohon shugaba Gbagbo a watan Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

An caji tsohon shugaban da laifin musgunawa jama'a, yanzu haka kotun kasa da kasa dake Hague kasar Holland ko Netherlands ce ke tsare dashi.

XS
SM
MD
LG