Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An dasawa tsohon mataimakin shugaban Amirka zuciya.


Yanzu haka tsohon mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney yana murmurewa, bayan ayi masa dashen zuciya a jiya asabar. Ofishin Cheney, yace shugaban yana dakin lura da mara lafiya sosai, da ake cewa intensive care, a asibitin Virginia. Watanin ashirin yayi yana jiran a samu zuciyar da za’a dasa masa.

Yanzu haka tsohon mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney yana murmurewa, bayan ayi masa dashen zuciya a jiya asabar.

Ofishin Cheney, yace shugaban yana dakin lura da mara lafiya sosai, da ake cewa intensive care, a asibitin Virginia. Watanin ashirin yayi yana jiran a samu zuciyar da za’a dasa masa.

Mukarabar Cheney, Kara Ahem tace Dick Cheney bai san ko zuciyar wa aka dasa masa ba.

Dick Cheney dan shekara saba’in da daya da haihuwa ya dade yana fama da ciwon zuciya. Tun lokacinda yake da shekaru talatin da bakwai da haihuwa zuwa yanzu, yayi fama da ciwon zuciya har sau biyar.

Na bayan bayan nan itace wadda ta faru a shekara ta dubu biyu da goma. A alif dari tara da tamanin da takwas jijiyoyinsa da suke ke jinni da iskar da muke shaka ta oxygen zuwa zuciya suka toshe, a saboda haka sai da likitoci suka yi aikin tiyatar canjar hanyar da jijiyoyin kebi ta kan zuciyarsa da ake cewa by pass surgery da turanci, sa’anan kuma an sa masa wani abu kamar balan balan a ciki babar jijiyar dake wuraren cinyar mutu wadda take zuwa har zuciya, domin ta bude jijiyoyin jinni dake kan zuciyar, ta yadda zuciyar ta samu jinni da iska. A shekara ta dubu biyu da daya kuma aka sa masa wata na’ura da ake cewa pace maker da turanci, domin ta taimaka wajen bugun zuciya, domin a cikin zuciya akwai abubuwan da suke sa zuciya tana bugawa, da tasa, suka samu matsala.

XS
SM
MD
LG