Lamarin ya auku ne a wani kauye mai suna Wuman, dake kusa da Andaha a karamar hukumar Akwanga, yayinda al’ummar Mada ke wani biki.
A cewar wani ganau da ya bukaci in sakaya sunansa, mutane goma sha shida ne ‘yan bindigar suka harbe har lahira.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jahar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini ya yi kira ga hukumomi su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata kisan, a kuma hukunta su.
Komishinan yada labaran jahar Nasarawa, Muhammad Jamil Zakari ya bayyana cewa, tuni gwamnati ta tura jami’an tsaro a yankin.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.