Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Daure Wani Mai Fafutuka a Bahrain Saboda Ya Soki Saudiyya a Twitter


Nabeel Rajab Dan Rajin Kare Hakkin Bil Adama Na Bahrain

An yanke wa wani mai fafutuka hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar a Bahrain, bayan da aka same shi da laifin yin kalamai marasa dadi a shafin Twitter.

Wata kotu a Bahrain ta yanke wa fitaccen dan rajin kare hakkin dan adam Nabeel Rajab, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari sakamakon wani rubutu da ya yi a shafin Twitter.

Rajab ya soki gamayyara dakarun da Saudiyya ke jagoranta kan hare- haren jiragen yaki da take kai wa a Yemen da kuma zargin cin zarafi da ake yi a gidajen yari.

Rajab ya taka muhimmiyar rawa a jagorancin zanga zangar magoya bayan masu rajin kare dimukradiyya a 2011 wacce ta mamaye fadin kasashe da ke yankin.

Tun daga lokacin ya sha dauri a gidan yari a lokuta da dama, haka kuma, kafin yanke hukuncin na yau Laraba tuni yana zaman daurin shekaru biyu sakamakon tsokacin da ya yi a yayin da ake gabatar da wani shirin talbijin.

Rajab shi ne shugaban Cibiyar Rajin kare hakkin dan adama a Bahrain, wacce bayan hukuncin da aka yanke masa yau, ta kira shari'ar da "wasa da shari'a"

Bahrain ta kasance mazaunin Sojojin ruwa na Amurka runduna ta biyar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nuart ta fadawa manema labarai a jiya Talata cewa Amurka ta yi Allah wadai da wannan mataki da kotu ta dauka akan Rajab.

Facebook Forum

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG