Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dorawa Alkalai da 'Yansanda Alhakin Cunkoson Gidajen Kaso


Wasu ke nan a gidan kason Jimeta dake jiran a yi masu shari'a
Wasu ke nan a gidan kason Jimeta dake jiran a yi masu shari'a

Yanzu haka akwai mazauna wadannan gidaje dubu biyu da hamsin da daya akasarinsu masu jiran shara'a wanda akadanganta da jinkiri da ake samu daga alkalai a daya bangaren da kuma su lauyoyi da jami'an 'yan sanda dake jankafa wajen gabatar da shaidu gaban kotu.

Tsohon alkali kuma mataimakin magatakardar babban kotun jihar Adamawa Barr. Husseini Duraki Kazir ya ce kamata ya yi idan lauya ko dansanda ya nemi a dage sauraron shara'a sau uku alkali ya kori karar bisa hujjar rashin kwakkwarar shaidu kuma ya sallami wanda ake tuhuma har sai lokacin da suka kammala tattara shaidu.

Limamin darikar Katolika Bishop Stephen Dami Mamza shugaban daya daga cikin kungiyoyi jinkai wa firsinoni ya nuna takaicinsa kan yadda fannin shara'a ke fifita masu hannu da shuni. yayin da lauya mai zaman kansa Barrister Sunday Wagira ke kallon lamarin daga kowane bangare ya jajirce wajen sauke hakkin da kundi tsarin shara'a ya ba shi.

Da yake kare jamiansa daga zargin yiwa shara'a karar tsaye. jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansanda ta jihar Adamawa DSP Othman Abubakar gani yake kamata ya yi a fadada gidajen yari saboda karuwar masu aikat laifuffuka.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG