Accessibility links

An Fara Samun Baraka A Jam'iyar APC, Jihar Kaduna

  • Grace Alheri Abdu

Tambarin jam'iyar APC

An sami baraka a jam'iyar APC a jihar Kaduna biyo bayan zaben Dr. Hakeem Baba Ahmed a matsayin sabon shugaban jam'iyar

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewa, an fara samun baraka a sabuwar jam’iyar APC biyo bayan nada Dr Hakeem Baba Ahmed da wadansu mutane biyu a matsayin shugaba da sakatare da kuma ma’ajin jam’iyar na jiha.

A cikin hirarsu da wakilin Muryar Amurka Isa Lawal Ikara Mr. Mataimaki Tom Maiyashi daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyar, ya bayyana bukatar sake salo.

Bisa ga cewar Maiyashi, idan ba an nemi hanyar dinke barakar aka kuma rungumi dukan ‘ya’yan jam’iyar ba, tana yiwuwa a sake komawa gidan jiya.

Shima Mallam Shu’aibu Lili daya daga cikin ‘ya’yan sabuwar jam’iyar CPC da ta narke ta koma APC. Yace an sha su sun warke saboda haka ba zasu yarda a sake maimaita kaura kuran da aka yi a lokutan baya a ya hana jam’iyar kai labari ba.
XS
SM
MD
LG