Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaben Shugaban Kasa A Zimbabwe


Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa Yana Kada Kuri'ar Sa

Murabus din shugaba Robert Mugabe a shekarar da ta gabata ya janyo hankalin mutanen da basu taba tsayawa takara ba, yasa suka shiga siyasa a wannan zabe mai dumbin tarihi da ake gudanarwa a yau Litinin, na farko tun samun 'yancin kasar Zimbabwe ba tare da Robert Mugabe a cikin 'yan takara ba.

'Yan takara guda biyu da suka fi kowa masoya basu kadai ne sababbi ba a wannan zabe. Dan takara mai zaman kanshi shine na uku a jerin 'yan takara da aka buga a katin zabe, biyo bayan dan takarar dake kan gaba, Emmerson Mnangagwa na jam'iyya mai mulki ZANU-PF,sai kuma dan adawa Nelson Chamisa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG