Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwakin Sojojin Amurka Na Cikin Jirgin Da Yayi Karo


Jirgin yakin Amurka da yayi karo

Amurka ta kawo karshen neman wasu mayakan ruwanta 7 da suka bace a bayan da aka gano gawarwaki a dakunan kwana na jirgin ruwan yakin Amurka mai suna USS Fitzgerald wanda ya ci karo da wani jirgin ruwan daukar kaya a dab da gabar kasar Japan jiya asabar da asuba.

Kwamandan runduna ta 7 ta mayakan ruwan Amurka, Vice Admiral Joseph Aucoin, ya fadawa ‘yan jarida yau lahadi cewa an kawo karshen aikin neman may6akan da suka bata. A fakaice dai, hukumomin Amurka suna nuna cewa babu wanda ya tsira da rai daga cikin mayakan bakwai, koda yake Vice Admiral Aucoin ya ki yace ko gawarwaki nawa aka gano har sai bayan an sanar da iyalan mamatan.

Aucoin yace ruwan teku ya shiga ya mamaye dakunan kwana a jirgin, kuma bangaren hannun daman a jirgin ya lotsa ciki.

Yace jikrgin ruwan yakin ya lalace sosai.

Yace da yawa daga cikin mayakan dake aiki a wannan jirgin ruwa suna barci a lokacin da ya ci karo da wani jirgin ruwan daukar kaya mai dauke da tutar Philippines mai suna ACX Crystal. Yace za a iya gyara jirgin ruwan yakin na USS Fitzgerald, amma zai dauki watanni.

Har yanzu babu wani bayani na yadda aka yi har jiragen ruwan guda biyu suka kara da junansu.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG