Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar da Addu'o'in Zaman Lafiya a Jihar Adamawa


'Yan gudun hijira a Adamawa.
'Yan gudun hijira a Adamawa.

Kama daga Lamidon Adamawa Dr. Muhammed Aliyu Mustapha zuwa mutanen gari duk suka yi cincirindo a masallatai daban daban har da na idi domin gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya wa jihar Adamawa da ma kasar baki daya.

Makasudin taron addu'o'in shi ne Allah ya kawo karshen ta'adancin da ya addabi yankin arewa maso gabas musamman jihar Adamawa.

Bayan musulmai da suka taru a masallatai haka ma mabiya addinin kirista suka yi a mijami'u daban daban inda su ma suka gudanar da addu'o'i.

Daliban makarantu da kuma kananan yara sun bi sahu wajen gudanar da addu'o'in Allah ya kawo karshen hare-haren da jihar ke fama dasu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG