Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Bitar Ayyukan Tsare Tsaren Zaben Jamhuriyar Nijer


A jamhuriyar Nijer shugabannin hukumar zaben kasar sun yi wata ganawa da wakilan jam”iyyun siyasa a karkashin inuwar majalisar warware rigingimun siyasa wato CNDP inda suka tattauna a game da inda aka kwana dangane da tsare tsaren zabukan da ke tafe.

Batun mutunta kason da dokokin kasa suka yi tanadi domin jinsin mata da nufin basu cikakkiyar damar shiga harakokin zabukan da ake shrin gudanarwa ta yadda zasu taka rawa sosai a harakokin gudanar da mulki na daga cikin muhimman batutuwan da taron na CNDP ya tattauna a kansu kamar yadda Dr Dita Idrissa kakakin kawancen MRN na jam’iyyu masu mulkin Nijer ya yi bayani.

Su ma dai jam’iyyu masu sassaucin ra’ayi da ake kira ‘yan baruwanmu sun yi na’am da wannan tsari na shigo da mata cikin sha’anin siyasa a fara daga batun basu tikitin zabe a cikin jam’iyyun siyasa, kamar yadda shugaban kawancen wadannan jam’iyyu, Malam Hambali Dodo ya bayyana.

Sake duba tsarin da ake gudanar da zabe a karkashinsa a Nijer na daga cikin bukatun da mahalarta wannan taro suka zo da su domin a cewarsu hanya ce da ka iya ba da damar dakile magudi sai dai wannan bukata ba ta sami shiga ba domin a cewar hukumar zabe dukkan wata kwaskwarimar doka a wannan lokaci da ake gab da soma fafatawa abu ne da ya sabawa doka.

‘yan adawa wadanda ke ci gaba da kauracewa dukkan wasu harakokin tsare tsaren zabe basu halarci wannan taro ba, matakin da ke nasaba da rashin halaccin da suka ce ya dabaibaye hukumar zabe ta CENI. A ranar 13 ga watan Disambar 2020 ne ake sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi yayin da za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki bayan makwanni 2 kacal wato 27 ga wata.

Saurari cikakken Rahoton Souley Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG