Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Fahintar Juna Tsakanin Manoma Da Makiyaya.


TARABA: Zanga-zangar makiyaya da manoma
TARABA: Zanga-zangar makiyaya da manoma

An gudanar da taron fahintar juna tsakanin manoma da makiyaya a masarautar Kontagora dake cikin jihar Niger.Fadar Mai martaba sarkin Sudan ne ta dauki nauyi wannan ganawar domin a samu fahitar juna.

Masarautar Kontagora dake cikin jihar Niger ta shirya taron tsakanin manoma da makiyaya domin gano hanyoyin warware matsalolin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.

Taron wanda aka gudanar a fadar mai martaba sarkin Sudan na Kontagora ya tattaro manoma da makiyaya dake yankin.

Masarautar tace ta damu ainun da ganin yadda ake yawan samun takon saka tsakanin manoma da makiyaya dake kai ga hasarar dukiya, wani lokacin har da rayuka.

Don haka tace akwai bukatar zaunawa domin cimma matsaya tare da ganin an kawo karshen wannan matsalar.

A cikin jawabin sa wajen taron mai martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Saidu Namaska ya ja kunnen bangarorin biyu da su daina daukar doka a hannun su kana ya shawarce su rika hankuri da juna.

Yace idan dabbobi suka shiga gonar ka abin yi shine ka sanar da hukuma idan har baku sasanta da mai dabbobin da suka yi maka banna ba.

Ga Mustafa Nasir Batsari da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG