Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Gunea


Zabe Guinea

Masu kada kuri’a sun yi layi a kasar Guinea yau lahadi da safe domin zaben shugaban kasa, inda shugaban kasar Alpha Conde ya sake tsayawa takara domin neman wa’adin mulki na biyu, tare da ‘yan takarar jam’iyun hamayya bakwai.

Ko da yake an sami fito na fito tsakanin magoya bayan jam’iyun dake hamayya da juna a farkon makon nan, a kasar Guinea, babu alamar rikici a Conakry lokacin da aka bude runfunan zabe.

Sai dai jam’iyun hamayya sun fara korafi kan zaben. A wata hira da babban shugaban jam’iyar hamayya Cellou Dalein Diallo ya shaidawa muryar Amurka cewa, bai amince da hukumar zaben ba. Yace shi da sauran ‘yan takarar shida zasu ki amincewa da sakamakon zaben idan har suka hakikanta cewa, an tafka magudi.

Dialo yace idan sakamakon zaben da hukumar zabe ko kuma kotun koli suka sanar, suka sabawa abinda jama’a suka zaba, ba zai amince da shi ba.

Jama’a sun shiga layi cikin tsanaki a mazabar unguwar Minierre dake birnin Conakry, inda wata jami’ar zabe tace zaben yana tafiya yadda ya kamata

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG