Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Manila Sakamakon Ziyarar Shugaba Trump


Trump
Trump

Aci gaba da ziytarar da shugaban Samurka Donald Trump a wasu Kasashen Asia yau lahadi ya sauka kasar Vietnam, kuma wasu 'yan kasr sunyi zanga-zangar nuna kyamar zuwan sa.

Shugaban Amurka Donald Trump yau ya sauka Manila domin halartan taro, tare da shugabannnin kasasshen kudu maso gabashin Asia.

Jirgin na shugaban Amurka ya sauka Manila ne kafin karfe 6 na yammacin can kasar.

Yako sauka ne bayan da kusan mutane da yawan su aka kiyasta sun kai 3,500, ‘yan kasar ta Filipino suka yi zanga-zanga zuwa ofishin jakadancin Amurka dake kasar.

Masu zanga-zangar suna tafe ne suna kuwwa suna cewa shugaban Trump ya kara gaba basa son ganin sa cikin kasar su, suna sukan gwamnatin na Amurka da cewa kasar ce wadda tayi wa kasar tasu mulkin mallaka shekaru 50 da suka gabata ba abinda take fata ganin sai yaki a wasu kasashen duniya.

Suna cewa sun san Amurka ce ke kaddamar da yake-yake cikin duniya, musammam ma ga kasashen duniya masu tasowa.

Sai dai dubban ‘yan sandar kwantar da tarzoma na kasar sunyi kokarin toshe hanyar da masu zanga-zangar zasu bi domin kaiwa ga inda aka shirya shiugaba Trump zai ziyarta amma hakan bai cimma nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG