Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zanga Zangar Kin Jinin Silman Batanci A Pakistan


Gungun 'yan Pakistan a wata zanga-zanga.
Dubban mutane sun yi jerin gwano a titunan babban birnin kasar Pakistan domin nuna fushinsu dangane da silman batanci kan addinin Islama.

Yan sanda sun ce kimanin mutane dubu goma sha biyar ne suka yi zanga zanga a Kirachi yau asabar ta nuna kyamar silman da aka hada a jihar California ta kasar Amurka.
Masu zanga zanga sun rika bayyana kalaman kin jinin Amurka.

Silman, mai lakabi da turanci “Innocence of Muslims” ya haifar da fushi a wadansu lokuta da zanga zangar da tayi sanadin asarar rayuka a kasashen Musulmi. An kashe mutane da dama a zanga zangar da ta hada da jakaden Amurka a Libya

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG