Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Hadin Kan Al’umma A Birnin Kwanni


A birnin Kwanni na jamhuriyar Nijer, an gudanar da wanni gagarumin taro domin inganta hadin kan jama’ar al’ummomi da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin manoma da makiyaya

A kowace shekara rikici kan barke a tsakanin makikaya da manoma, lamarin da ke sanadiyyar rayuka da kuma asarar dukiyoyi da dama a dukan bangarorin biyu.

Yayin da yake jawabin bude taron, gwamnan jihar Tawa, Mousa Abdulrahaman, ya bayyana cewa wannan niyya da jama’ar suka dauka abar yabawace kwarai domin idan babu kwanciyar hankali da hadin kai a tsakanin al’umma, babu yadda kasa zata ci gaba.

Alhaji Umarou Wandara, shugaban kwamitin da ya shirya ganawar tsakanin al’ummomin Kwanni, ya ce lallai kwalliya ta biya kudin sabulu domin a cewarsa, yadda jama’a suka nuna goyon baya da halartar tattaunawar ya nuna yadda suka yi na’am da wannan kira.

Hajiya Rabi, ‘Yar majalisar dokoki ta kasa mai wakiltar birnin Kwanni, ta ce suma zasu kawo nasu kokarin domin nuna goyon baya da kuma tallafawa matasa domin sama masu ayyukan yi, da karfafa zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, ne maudu’in tattaunawar.

Ga cikakken rahoton Haruna Mamman Bako Daga Birnin Kwanni.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG