Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da Wanda Ya Kai Hari A Filin Jirgin Saman Florida


Gwamnan jahar Florida, Rick Scott, ke jawabi kan harinn.

Mutumin nan da ya kai hari a wani filin jirgin sama a Florida ya gurfana gaban kotu. Cikin tuhumce-tuhumcen da ake masa har da na kashe mutane biyar da kuma raunata wasu.

A yau Litinin dan bindigar nan da ya kashe mutane biyar a filin tashin jiragen Florida zai bayyana a karon farko a gaban kotu.

A ranar Asabar din da ta gabata aka tuhumi Estaban Santiago da aikata wannan ta’asa wacce ta yi sanadin mutuwar mutane, ta kuma iya yiwu wa ya fuskanci hukuncin kisa ko kuma daurin rai-da-rai.

Amma yayin da hukumomin ke ta neman dalilin da ya sa ya kai wannan hari, ‘yan uwan Santiago, sun ce ya samu matsalar tabin hankali, tun bayan da ya kwashe watanni 11 ya na wa Amurka yaki a kasar Iraqi.

Bryant Santiago, dan uwane ga Estaban, ya ce:

“Wannan ai laifin hukuma ne, ba kowa bane zai je wajen gwamnatin ya na neman taimako, amma kuma idan irin wannan mummunan lamari ya faru, sai a gano cewa ba mutum bashi da lafiya, akwai abin daya fi mutum ya kai kansa y ace bashi da lafiya ya na neman taimako?”

Sai dai duk da haka, hukumar FBI mai binciken manyan laifuka ta ce har yanzu, ba ta tsame batun ta’addanci a wannan hari ba, wanda aka kai a wajen daukan kayayyakin filin tashin jiragen Fort Lauderdale dake jihar Florida.

XS
SM
MD
LG