Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Haifi Birrai Biyu a New York


Daya daga cikin jariran Gwarilla

​Wani gidan ajje dabbobi a birnin New York na bukin haihuwar wasu birrai guda biyu, wato nau’in gwarilla a turance, irin marasa wutsiya.

Wadannan sune karo na farko da aka haifa a gidan zu dake mallakar kungiyar kiyaye dabbobin dawa dake unguwar Bronx tun shekara ta 2006.

Jami’an gidan ajje dabbobin basu fadi jinsu birran ba tukkunna.

Dukkaninsu dai basu fi kilogram biyu biyu ba.

ama dai irin wannan nau’uka na birrai idan suka girma matansu na kai kilogram 115, maza kuma har zuwa kilogram 200.

Jariran gwarilla na zama ne a hannun iyayensu mata na tsawon watanni 4 a farkon rayuwarsu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG