Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Har Lahira Wani Kwamandan Soji A Katsina


Yan bindiga
Yan bindiga

Lamarin ya faru ne inda mamacin, wanda Manjo ne a rundunar sojin Najeriya, ke amsa kiran gaggawa na gudanar da aikin tsaro.

ABUJA, NAJERIYA - An kashe wani babban kwamandan soji a wani harin kwantan bauna da yammacin ranar Alhamis a jihar Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Malali da ke karamar hukumar Kankara na Jihar Katsina.

A cewar majiyoyi masu inganci, babban jami’in sojan na kan hanyarsa ne domin tallafa wa dakarun yankin da suka dakile harin, yayin da ‘yan bindiga suka tare motarsa.

“Yankin da ke kan titin Zangon Pawwa, inda Malali yake, yana fama da ayyukan ‘yan bindiga,” in ji wata majiya.

“Yawancin lokuta rundunar sojin sukan naimi taimako da karin karfi daga sansanin sojin da ke Dan Ali, wanda marigayi Manjo ke kokari nan da nan don kawo agaji”

kwamandan yana tafiya ne a cikin motar Hilux maimakon motar yaki mai ɗaukar makamai, wanda mai yiwuwa ba a samu ba a lokacin.

Majiyar ta kara da cewa "Maharansa sun yi masa kwanton bauna inda suka harbe shi har lahira."

A yayin da aka samu gawar sa, an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin jami'an soji da 'yan bindigar, lamarin da ya yi sanadin jikkatar wasu da dama ciki har da wani jami'in da shi ma aka harbe.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG