Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Belgium Jami'an Tsaro Sun Bunduge Wani Dan Harin Ta'addanci.


Belgium inda aka sami wata fashewa.

Hukumomi a kasar Belgium sun ce sun dakile wani harin ta'addanci a jiya Talata.

Hukumomi a kasar Belgium sun ce sun dakile wani harin ta'addanci a jiya Talata a lokacin da jami'an tsaro suka harbe wani mutumin bayan tashi wani bam mai ban tsoro.

Kakakin ofishin lauyan gwamnatin tarayya Eric Van der Sypt yace sojoji sun gaggauta fin karfin wani wanda ake zaton shine ya tada bam din a wata babban tasha bayan pashewar. Ya kuma kara da cewar mutumin da ake zaton ya kai harin ya mutu.

Van der Sypt yace an dauki wannan hari a matsayin aikin ta'addanci.

Babu wanda yaji rauni baya ga wanda ake zaton shi ya kai harin da aka kashe. Al'amarin ya faru da misalin karfe tara na dare agogon can, bayan raguwar cunkoson mutane.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG