Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Horar Da ‘Yan Kato Da Gora a Shiyar Arewa Maso Gabashin Najeriya


‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen zirga-zirga a birnin Yola.

A kokarin neman mafita kan matsalolin tsaro a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya, hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada horo na musamman wa wassu ‘yan kato da gora.

Kungiyar ‘yan kato da gora ta Civilian JTF da Vigilante daga jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe, sune suka sami horon yadda za su taimaka wa kokarin gwamnati wajen yaki da Boko Haram da inganta zamanta kewar al’ummomin yankin.

Cibiyar koyar da shugabanci da zama ‘dan kasa na gari, dake birnin Jos, ita ce ta horar da matasan su dari biyar da saba’in da bakwai (577).

Darakta janar na cibiyar, Mr Jonah Bawa, ya ce sun horar da matasan ne kan yadda zasu yi mu’amula da mutane da sauya tunaninsu, don taimaka wa kasarsu.

Wasu da suka sami horon sun bayyana cewa zasu yi amfani da abin da suka koya don samar da zaman lafiya.

Mai hada shirye-shirye a kungiyar Civilian JTF na jahar Borno, Abba Aji, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kula da wadan da suka sadaukar da rayukansu wajen samar da tsaro a jihar.

Wakilin hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mathew Alao, ya yi fatan wadan da suka sami horon za su yi amfani da abin da suka koya wajen sasanta al’umma da inganta tattalin arzikin kasa.

Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG