Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Jigilar Alhazai A Najeriya


Mahajjata na tsaye a wani sansanin alhazai su na jira a yi mu su gwajin cutar Ebola kafin su shiga jirgin saman zuwa Saudiyya, a ranar goma sha takwas ga watan satumba shekarar dubu biyu da goma sha hudu.

Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa’ad Abbubakar da Mai alfarma Sarkin Kano Sanusi na biyu sun kaddamar da jigilar alhazan bana.

A cikin jawabinsa wajen kaddamarwar da aka gudanar a garin Kaduna, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya yi kira ga gwamnatoci su rika taimakawa mabukata, yayinda kuma ya gargadi mahajjata subi umarnin hukumomi a kowanne mataki.

Sarkin Kano, Mal Sanusi na biyu wanda zai jagoranci kwamitin gwamnatin tarayya a aikin hajin bana, ya hori mahajjata suji tsoron Allah wajen gudanar da aikin hajji tare kuma da addui’ar zaman lafiya a Najeriya.

A cikin jawabinsa, mai masaukin baki, gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufa’I wanda kuma ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari, shima ya jadada bukatar kiyaye doka da oda yayin gudanar da ayyukan hajji.

Ana kyautata zaton mutane dubu saba’in da shida ne zasu gudanar da aikin hajjin bana daga Najeriya, da kuma jami’ai dari takwas da hamsin, yayinda kamfanoni shida zasu yi amfani da jirage goma sha uku wajen jigilar alhazai.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Yakubu Birnin Yaro ya aiko daga Kaduna, Najeriya.

Rahoton aikin hajjin bana-3:06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG