Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kaddamar da sabon asibitin jinyar mata jihar Madarunfa Jamhuriyar Niger


Wata mace a kwance ana yi mata jinya

Jakadiyar Amurka a jamhuriyar Niger Bisa Williams ta kaddamar da wani asibitin jinyar mata masu yoyon fitsari a jihar Madarunfa.

Jakadiyar Amurka a jamhuriyar Niger Bisa Williams ta kaddamar da wani asibitin jinyar mata masu yoyon fitsari a jihar Madarunfa.

Da take kaddamar da asibitin, jakadiyar Amurka ta bayyana cewa kasar Amurka zata ci gaba da tallafawa yunkurin inganta lafiyar mata.

Asibitin da wata kungiyar agaji ta kasa da kasa da ake kira SIM International and Worldwide festula ta gina mai gadaje arba'in da biyu, wanda zai rika jinyar mata kyauta, tuni ya fara aikin tiyata bayan yiwa mata hamsin rajista.

An kuma karfafa mata su garzaya asibitin domin samun kula duk lokacin da bukatar haka ta taso.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG