A wani yunkuri na gwamnatin kasar Nijer, don yaki da rashin aikinyi, talauci, zauna gari banza, da kuma neman tsaftace garuruwan kasar. A ranar 10 ga watan Nuwamba, ta kaddamar da wani shiri. A tabakin comadan kare gandun daji a birnin Maradi Mohamda Lauwali Hami, ya ce rashin tsaftache gari na haddasa abubuwa da dama, yawanci ma idan ka duba irin cututuka da a ke fama da su suna da nasaba da rashin tsaftace muhalli.
Don haka shiyasa gwamnati ta fito da wannan shirin don a tabbatar da tsaftar muhalli kana kuma a sama ma mutane da dama aikin yi. Wannan wani tsari ne da mutane zasu bazama cikin kasa don samo ledoji da sauran abubuwan da ke haddasa taruwan ruwa da hana magudanai wucewa, wanda zasu kawo sai a gwada nauyin kamun a biyasu, dai dai aikin ka dai dai kudinka wanda kowace kilo daya ana biyan dala 40 na sefa.
Ya kuma jawo hankalin al’umah da su kauracema yadda matattun dabbobi a cikin gari, don ba’a san wane irin ciwo ya kashe wannan dabbar ba wanda zai iya cutar da al’umah. Ta bakin wasu masana suna ganin wannan wani abun alfanu ne ga kasar saidai suna ganin yakamata ace an dauki matakan kare lafiyar masu wanna aiki. Ko da yaushe sukayi wannan aikin to kamin a biyasu hakkinsu to a tabbatar da cewar an basu sabulun wanke hannu don kauce ma wasu cututuka.