Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Kotu Ta Musamman Da Za Ta Binciki Jami'an Soji 21


Kotun Soji A Maiduguri Tana Shari'ar Wasu Sojoji
Kotun Soji A Maiduguri Tana Shari'ar Wasu Sojoji

Kwamandan rundunar soja na "Operation Lafiya Dole" da ke shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Manjo Janaral Benson Akinroluyo, ya kaddamar da wata kotun soja ta musamman da za ta hukunta wasu Jami’an soja 21 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

An dai kaddamar da wannan kotun ce a barikin soja da ke Maimari a garin Maiduguri, karkashin jagorancin Manjo Janaral Abdullahi Ibrahim, Wanda zai kasance shugaban wannan kotun, da ta hada da wasu mambobin kotun.

Kwamandan kotun ya ce wannan kotun za ta gudanar da ayyukanta ne ba tare da wani katsalandan ba, kuma za su tabbatar cewa wannan kotun ta yi aikinta cikin adalci ba tare da goyon bayan, ko kuma daurewa wani bangare gindi ba.

Kwamandan ya ce mutane 21 ne dai ake Saran za’a yi masu shari'a, da wadanda kuma suka aikata laifuffuka daban-daban, sai dai ba’a bayyana irin laifuffukan da ake zarga Jami’an sojan da aikatawa ba.

Sai dai a baya irin wannan kotun sojan na musamman da aka kafa a garin Maiduguri ta yanke hukunci ga wasu Jami’an sojan a baya, akan wasu laifuka da suka hada da na fede, da cin zarafin jama’a, da arcewa a bakin aiki, da kinsan kai da gangan ga fararen hula, da dai wasu laifukan da suka sabawa tsarin mulkin kasar.

Ga cikakken rahoton wakilin muryar Amurka Haruna Dauda Biu daga Maiduguri

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG