Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari A Fadar Gidan Sarautar Saudi Ta Birnin Jiddah


Saudi Trump Mission to Dazzle

Wani dan tarar aradu da ka ya kai hari a Fadar Al-Salaam ta gidan sarautar Saudiyya da ke birnin Jidda. To amma kamar yadda ya kashe dogarawan tsaron Fadar biyu, shi ma an hallaka shi.

Jiya Asabar Ofishin Jakadancin Amurka da ke kasar Saudiyya, ya gargadi Amurkawa da su yi kaffa-kaffa da wuraren da ke kusa da Fadar Al Salaam, bayan rahotanni sun nuna cewa an kai wani hari wurin.

Ministan Cikin Gida na Saudiyya ya fadi jiya Asabar cewa an kashe wasu dogarawan tsaron fadar biyu 'yan asalin Saudiyya baya ga wasu uku da su ka ji raunuka, bayan da wani mutum ya tuko wata mota zuwa mashigar sashin yamma ta Fadar Gidan Sarautar Saudi a Jeddah, ya shiga bude wuta.

Wani mai magana da yawun Ma'aikatar ya ce dogarawan tsaron fadar sun bindige maharin har lahira.

Mai magana da yawun Ma'aikatar ya ce maharin dan asalin kasar ta Saudiyya ne, mai suna Mansour al-Amri, dan shekaru 28 da haihuwa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG