Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari A Wani Coci Dake Kudancin Cairo


Suicide Bombers Attack Pakistani Church Ahead Of Christmas GRAB

Wani dan bindiga yakai hari a wani coci dake birnin CVairo kuma ya kashe mutane 9 ciki ko harda dan sanda guda,kana mutane biyar sun samu rauni.

Wani dan bindigan da ba a san ko wanene ba ya bude wuta a wajen wani coci, dake kudancin birnin Cairo.

Cocin dai yana kusa da wani shago ne mallakan mabiya addinin kirista.

Kuma ya kashe a kalla mutane 9 ciki ko har da dan sanda guda.

Sai dai mahukuntar kasar ta masar sunce na take aka harbe wannan maharin.

An Kashe sni ne ta musayar wuta dashi a jiya jumaa a kusa da cocin da ake kira Mary Mina church dake gundumar Helwan.

Mai Magana da yawun maaikatar kiwon lafiya na kasar Khaled Megahed yace mutane biyar ne suka samu rauni ciki ko har da wani Dan sanda.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wanna harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG