Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai hari akan coci a jihar Anambra arewa maso gabashin nigeria.


Coci

An kashe mutane 12 a harin da wani dan bindiga yake akan coci a jiar Anambara dake kudu maso gabashin Nigeria.

Hukumomi a Najeriya sun ce mutane 11 sun mutu, sa'anan wasu 18 sun samu munanan raunuka a wani harin da aka kai wata majami'a a kudu maso gabashin kasar.

Gwamnan jahar Anambra Willie Obiano, ya ce wannan harin ya samo asali ne daga wani rashin jituwa tsakanin wasu 'yan garin da ke zaune a wata kasar waje.

Ba kasafai ake kai hari akan coci a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke da rinjayen mabiya addinin Kirista,

Wakilin sashen Hausa Lamido Abubakar Sokoto ya aiko da rahoton cewa, wasu alkaluma na fadin cewa an kashe kusan mutane 100 a harabar cocin, wasu kuma suna cewa mutane 50 ne suka rasa rayukan su.

To amma alkaluma na hukuma na nuna cewar mutane 12 ne suka mutu, mutane 27 kuma suka jikatta.

Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Anambara Garba Umar ya fadawa wakilin sashen Hausa cewa wani dan bindiga ne ya kai wa cocin hari. Kuma a harbe harben da yayi, nan take aka tabbatar ya kashe mutane 8. Daga baya kuma aka debi wasu da yawan gaske aka kai su asibiti.

Yace ;labarin da suke dashi a yanzu, ajwai mutane 12 wadanda aka tabatar cewa sun mutu, sa'anan mutane 27 ne aka kwantar a asibitoci.

Haka kuma kwamishin 'yan sandan yayi bayanin cewa ba wai 'yan Boko Haram bane suka kai harin. Domin tunda farko wasu sun fara yayatawa jita jitan ne yan Boko Haram ne suka harin. Yace babu ruwan 'yan Boko Haram ko Fulani a harin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG